Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gabanin zaɓen 2027, Ƙungiyar Northern Democrats (LND) ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ta bayyana cewa ta na shirin rikiɗewa zuwa jam’iyya.
Ƙungiyar ta kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki da jam’iyyar adawa ta PDP da gazawa wajen cika burin ƴan Najeriya, tare da neman haɗin gwiwa da ga ƙungiyoyi a Kudu don kafa jam’iyya mai ƙarfi.
Daily Trust ta rawaito cewa mai kula da harkokin LND na ƙasa, Dokta Umar Ardo, a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi, ya bayyana cewa LND tana matsayin haske na ceto ƙasa da ke kan hanya, inda ya jaddada cewa ƙungiyar ta dogara ne akan ƙa’idojin dimokraɗiyya kuma tana da niyyar sake gina ƙasa.

Ya ce tarin matsalolin da su ka addabi Najeriya, ciki har da talauci mai tsanani, rashin tsaro, rashin daidaito, cin hanci da rashin ci gaba a tattalin arziki, duk suna da alaƙa da gazawar shugabanci a ƙasar.
Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya rabawa sabbin kwamishinoni ma’aikatu
Ardo ya bayyana cewa shirin sauya ƙungiyar zuwa jam’iyyar siyasa ya biyo bayan kira daga tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Salihu Mohammed Lukman, a cikin saƙon sabuwar shekarar da ya fitar kwanan nan, inda ya soki gazawar tsarin siyasar Najeriya, musamman “Rashin dimokraɗiyya da rashin ƙwarewa da suka mamaye APC da PDP.”