Kungiyar Zango Educational initiative forum wadda ke rajin tallafawa ilmin matasan unguwar zango dake karamar hukumar birnin Kano ta gabatar da wani gangamin taro domin wayar da kan matasa muhimmancin ilimi.
Da yake jawabi a wajan taron shugaban kungiyar Dr. Usman Umar Zango ya ce sun shirya taron ne da niyar lalubo hanyoyin tallafawa matasan yankin akan harkokin da su ka shafi ilmi, domin ilimin shi ne hanya daya tilo da za ta mayar da matasa hanya madaidaiciya.
” A kowanne lokaci shi matashi yana bukatar a rima yi masa jagora hakan shi zai sa a gano inda ya dosa, inda yana kan daidai sai a yaba masa a kara masa kwarin gwiwa, idan kuma ya baude sai a dawo da shi kan hanyar domin ya amfani kansa sannan ya amfani al’umma”. Inji Dr. Usman Umar Zango

Ya ce koyar da matasa ilimi da shirya irin wadannan laccoci na daga cikin muhimman aiyukan kungiyar Wanda take yi ga matasa Maza da mata na unguwar Zango.
” Kasancewar matasa su ne kashin bayan cigaban kowacce al’umma akwai bukatar al’ummar kowacce unguwa su rika shiryawa matasan su wata bita lokaci zuwa lokaci ko dan matasan su fahimci kansu, saboda sun su amfanar da jama’a”. Inji Dr Usman
Dubun wani matashi da ya sace yaro dan shekaru 2 ta cike a Kano
Shi ma a nasa bangaren guda daga cikin dattawan unguwar ta zango mallam shu’aibu Idris ya ce suna yin duk abun da ya kamata don nunawa matasan unguwar abubuwan da suka dace.
“Babban burinmu shi ne matasan unguwar su yi fice akan ilmin, ina kuma yin kira ga dattawan kowacce unguwa dake jihar Kano da su yi koyi da abun da wannan kungiya dake Zango ta yi domin kauda hankalin matasa daga aiyukan bata gari”. Malam Shu’aibu Idris
Muhammad Garba matashi ne daga cikin matasan unguwar yace matakan da wannan kungiya take dauka za su taimaka sosai wajen inganta rayuwar matasan unguwar Zango.
“Tabbas iyayenmu suna son ganin mun zama wadannan za a yi alfahari da su, don haka dole mu basu goyon bayan da hadin kan da ya dace domin cikar wannan burin nasu na ganin kowanne matashi a unguwar Zango ya sami ingantaccen ilimi”. Muhd Garba.
Taron dai ya gudanane afarfajiyar unguwar ta zango Dake bayan asibitin murtala inda ya samu halartar Manyan unguwar da kuma wasu daga makwabta.