Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Shugaban rukunin jami’o’in MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru 62 da haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Farfesa Gwarzo ya ce “Dukkan godiya ta tabba ga Allah Madaukakin Sarki da ya raya mu cikin koshin lafiya har muka shaida wannan gagarumin biki na murnar zagayowar ranar haihuwarka.”

Manyan nasarorin da ka samu ya zuwa yanzu a fannonin ilimi, lafiya, da samar da ababen more rayuwa ya nuna yadda kake da kishi da son ci gaban jihar Kano.
Abba@62: Tabbas Kanawa za su jima suna morar Salon mulkinka – Sakon Kwankwaso ga Gwamnan Kano
“Ya kamata sauran gwamnoni kasar nan su yi koyi da yadda kake sadaukar da kai don hidimtawa al’ummar Kano, lallai tarihi zai da dade yana tunawa da hidimar da ka yi wa Kano. Tabbas Kano ta yi sa’ar samun ka a matsayin gwamna.” Inji Farfesa Gwarzo
Farfesa Gwarzo wanda shi ne wanda ya assasa Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria, Niger, Franco-British International University Kaduna da Canada University of Nigeria da ke Abuja ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya yi wa gwamna jagora wajen sauke nauyin da ke kansa, ya kuma kara masa basira da koshin lafiya domin ya cigaba da hidimtawa al’umma.