Daga Sani Idris maiwaya
Jagoran Jam’iyyar NNPP na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yana da salon mulkin da gwamna Abba Kabir Yusuf yake yi a Kano da irin cigaban da ya kawowa jihar.
“Babu shakka cikin watannin 19 da zamanka gwamna ka kawo wa jihar Kano cigaba mai tarin yawa a fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar jihar, tabbas salon mulkinka abun yabo ne”.
Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a sakonsa na taya gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru 62 da haihuwa.

Ya ce shekaru 62 da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a duniya cike suke da albarka da sadukarwa musamman wajen cigaban jihar Kano da kasa baki daya.
“Salon mulkinka na sauraren koke da korafin al’ummar jihar Kano da kake mulka , ya nuna tsantsar kwarewarka wajen iya tafiyar da harkokin mulki wanda kuma haka ake bukata ga kowanne shugaba nagari”. Inji Kwankwaso
Hukumar Tace Fina-fina ta Kano ta Dakatar da Babbar Jaruma a Kannywood
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wanda shi ne ya yiwa Jam’iyyar NNPP takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya yiwa gwamnan fatan samun karin shekaru masu albarka don al’umma su cigaba amfana daga gare shi .