Sarki Aminu ya dawo Kano bayan ziyarar da ya kai ƙasar Egypt

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Dubbunan al’ummar jihar Kano ne suka tari Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero Bayan dawowarsa daga kasar Egypt a wata ziyarar aiki da ya kai.

Masoya sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero fitar farin dango tare da cika tituna domin yin lale marhabun da dawowar Sarkin gida lafiya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran sarkin Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Talla

A kalla dai an shafe awanni masu yawa daga filin sauka da tashi na Malam Aminu Kano (MAKIA) zuwa gidan Mai Martaba Sarkin dake Nassarawa sakamakon yawan al’umar da suka tareshi babu masaka tsinke.

Idan dai za’a Iya tunawa Kimanin makonni biyu Kenan Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yabar Kano zuwa kasar ta Egypt domin ziyarar aiki.

A lokacin ziyarar ne ma Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin kungiyoyi daban daban na Yan Najeriya dake zaune a kasar ta Egypt.

Ban da talauci ba abun da kudirin dokar harajin zai karawa yan Nigeria – Gwamnatin Kano

Kazalika Sarkin ya gana da jami’ai na Gwamnatin Kasar da mambobin diflomasiya da daidaikun mutane wadanda suka tattauna akan harkokin kasuwanci da tattalin arziki da Kuma cigaban jihar Kano da Najeriya.

Bayan saukar sa a fadarsa dake Nassarawa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa dumbin al’umar da suka tareshi tareda yimusu addu’ar fatan alheri.

Alhaji Aminu Ado Bayero yayi amfani da wannan dama wajan Kara Jan hankali matasa su cigaba da kasancewa masu da’a da ladabi da biyayya da son junansu da Kuma Zaman lafiya.

Ya sake yabawa al’uma bisa yadda suka fito cikin ladabi da nutsuwa domin nuna godiyarsu ga Allah da nuna farin cikinsu bayan dawowarsa daga ziyarar aiki a kasar Egypt.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...