Gwamna Yusuf ya taya al’ummar Kano murnar shigowa sabuwar shekarar 2025

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sakon taya al’ummar jihar Kano murnar shigowa sabuwar shekara, inda ya bayyana fatan samun ci gaba a wannan Shekarar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Jaridar Kadaura24 a ranar Laraba.

A cikin sakon nasa, Gwamnan ya yaba da juriya da hakurin da mazauna Kano suka nuna wajen tunkarar kalubalen da suka fuskan a 2024 tare da tabbatar musu da jajircewar sa na ganin ya samar da ci gaba mai ma’ana a 2025.

Talla

β€œina yiwa duk yan jihar kano Barka da shigowa sabuwar shekar. Ina fatan Shekara ta 2025 ta zama shekarar aminci, zaman lafiya, wadata, da karin hadin kai,” in ji Gwamnan, inda ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin inganta rayuwar kowane dan jihar.

Ya kara da cewa gwamnatin sa ta yi kokari matuka wajen ganin an amince da kasafin kudin shekarar 2025 a kan lokaci, yana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na habaka ci gaba a fadin jihar.

Tun da kasafin kudi zai fara aiki a yanzu, Gwamnan ya nuna kwarin gwiwar cewa Kano za ta samu ci gaba a fanni samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da noma a shekara mai zuwa.

Jerin Aiyuka 24 da Abdulmumini Kofa ya yi a kananan hukumomin Kiru da Bebeji a 2024

Gwamnan ya bayyana shirye-shiryensa na kammala ayyukan tituna da ake ci gaba da yi a jihar, da fadada cibiyoyin kiwon lafiya, da inganta harkar ilimi, da tallafa wa manoma da kayan aiki don bunkasa noman abinci da rage tsadar kayan abinci.

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin sa na bunkasa rayuwar matasa da mata ta hanyar koya musu sana’o’i da kuma kara samar da rance ga kanana da matsakaitan β€˜yan kasuwa don ciyar da tattalin arzikin jihar gaba.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da baiwa gwamnatinsa hadin kai da goyon baya a kudirinsa na kawo cigaba jihar.

Ya yi fatan shekarar 2025 za ta kasance shekara wacce za a sami sauyi, wanda zai samar da ingantacciyar rayuwa da samar da damammakin tattalin arziki a kowane lungu da sako na jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related