Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya a Jihar Kano kan laifin aikata kisa a wurin bikin Ιaurin aure.
Babbar Kotun Jihar Kano ta kuma yanke wa matashin mai suna Abba Suleiman hukuncin Ιaurin shekara biyar a gidan yari kan laifin hada baki da aikata laifi.

Mai Shariβa Amina Adamu ta yanke wa Abba hukuncin ne tare da wasu abokansa da suka tsere, bayan samun su da laifin caka wa wan mai suna Iliyasu Tasiβu wuka har lahira a yayin bikin auren.
Kasafin 2025: Engr. Sani Bala Tsanyawa ya gabatar da wasu muhimman batutuwa guda biyu a majalisa
An fara gurfanar da Abba a kotun ne 2019 bayan an kama shi yana ΖoΖarin hana kai wata amarya dakin mijinta a unguwar Sauna Kawai da ke Ζaramar Hukumar Nassarawa a jihar.
A lokacin taΖaddamar ce wanda a ake zargin ya aikata kisan da aka yanke masa hukumci a kai.
Bayan sauraron lauyoyi da shaidun masu kara da wanda ake Ζara, AlΖali Amina Adamu ta ce masu kara sun gabatar da gamsassun dalilai da ke tabbatar da laifin wanda aka gurfanar don haka ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya da kuma Ιaurin shekara biyar.
Daily trust