Kasafin 2025: Engr. Sani Bala Tsanyawa ya gabatar da wasu muhimman batutuwa guda biyu a majalisa

Date:

Daga Sadiya Ahmad

 

A kokarinsa na ganin an sanya tare da samar da abubunwan da za su kyautata rayuwar al’ummarsa , dan majalisar tarayya mai wakilar kananan hukumomin Ghari da Tsanyawa Engr Sani Bala Tsanyawa ya gabatar da wasu muhimman batutuwa da suke damun al’ummar Nigeriya musamman arewa baki daya.

A yayin muhawarar kasafin kudin shekara ta 2025, Engr Sani Bala yayi magana akan wasu muhimman batutuwa guda biyu da suka shafi Najeriya.

Talla

Da farko ya gabatar da batun inganta matakan tsaro don hana lalata layukan dake dakon wutar lantarki a fadin Nigeriya. Lallacewar layukan wutar da ake yawan samu na haifar da gagarumin koma baya da haifar da matsaloli daban-daban musamman ta fuskar tattalin arzikin da tsaron kasa.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a wanann shekarar da muke bankwana da ita kusan sau 12 aka sami katsewa ko saukar babban layin wutar lantarki na kasa wanda hakan babbar barazana ce ga masu kananan masana’antu.

Rushe Daula Otel: Kotu Ta Ci Tarar Gwamnatin Kano

Na biyu, Engr. Sani Bala ya gabatar da batun kalubalen da ke tattare da lodin da manyan motoci ke na kayan abinci a Kasuwar Dawanau, wanda kuma suke fitar da shi daga kasar zuwa makwabtan kasashe.

Kayan Abinchin da Ake fitar da su zuwa makwabtan kasashe sun hadar da gero, masara, Dawa da wake, wanda hakan ke haifar da ƙarancin abinchi da kuma tsadarsa a Nigeria.

Dr. Engr. Sani Bala ya ce Idan majalisar ta yi abun da ya dace akan wadancan batutuwa al’umma zasu sami saukin al’amuran rayuwa.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar larabar da ta gabata ne Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekara ta 2025 a gaban hadakar majalisar ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...