Yan Nigeriya sun shiga halin rashin tabbas da yan majalisa suka rera wakar Tinubu

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Al’ummar Nigeria sun shiga ruɗani tun lokacin da suka jiyo yan majalisar tarayya da na Dattawa suna rera taken Tinubu ” Tinubu Anthem” lokacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tashi domin gabatar da jawabinsa gabanin gabatar da kasafin kudin shekara ta 2025.

Taken Tinubu wato “Tinubu Anthem” wani take ne da yan Siyasa masu goyon bayan tafiyar Tinubu suke yi musamman idan an zo taron siyasarsu.

Talla

A wani faifen bidiyo na zaman majalisun biyu da jaridar Kadaura24 ta gani, mun jiyo yan majalisar na rera wakar da ke nuna cewa za su tsaya akan duk abun da Tinubu ya umarce su tare da kare muradunsa.

Gwamna Kano ya kara mutum 1 cikin kwamishinonin da Majalisa ta tantance

Abun da yan majalisar su ka yi yasa shakku a zukatan wasu daga cikin al’ummar Nigeriya, musamman game da makomar kasar da yan ƙasar.

A wannan rana ce dai Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekara ta 2025 ga hadakar majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...