Kotun Ƙoli ta kori ƙarar da ke neman ta sauke Tinubu daga shuagaban Nigeria

Date:

 

 

Kotun Ƙolin Nijeriya, a yau Litinin ta yi watsi da karar da ke neman ta tsige shugaba Bola Tinubu daga mukaminsa.

Kotun kolin, a wani mataki na bai-ɗaya da wasu alkalai biyar su ka yanke, ta kuma ci tarar Naira miliyan 5 akan wanda ya shigar da karar, Cif Ambrose Owuru, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Hope Democratic Party, HDP, a zaben 2019.

Kwamitin wanda mai shari’a Uwani Musa Abba-Aji ta jagoranta, ya kuma gargadi ofishin gudanar wa na kotun koli da kada ya sake karbar duk wata ƙara daga mai karar.

Talla

A shari’ar da ya shigar kai tsaye a kotun koli, Owuru, a cikin wasu zarge-zarge, ya yi zargin cewa shugaba Tinubu ma’aikaci ne na Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA), matsayar da ya ce ta sa shi ya sanya shi zama shugaban kasa.

Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano ya aike da suneyen wadanda zai nada Kwamishinoni ga Majalisar jihar

Hakazalika mai shigar da karar ya bukaci kotun kolin da ta haramtawa Tinubu takara bisa zargin ya taba mayar da dala 460,000 ga gwamnatin Amurka a shari’ar da ta shafi miyagun kwayoyi.

Ya kuma roki kotun koli da ta yi amfani da sashe na 157 na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, sannan ta kori Tinubu daga mukaminsa saboda kasancewarsa karkashin ikon hukumomin kasashen waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...