Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya cire mataimakinsa Kwamaret Aminu Abdussalam Gwarzo daga kwamishinan Ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar, Inda aka mayar da shi kwamishina a ma’aikatan Ilimi mai zurfi ta jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.
Sauran wadanda gwamnan ya sauyawa wuraren aiki sun haɗar da Hon. Mohammad Tajo Usman wanda aka mayar da shi ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu daga kimiyya da fasaha sannan Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata daga ilimi mai zurfi aka mayar da shi ma’aikatar kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire.

Sauran su ne Hon. Amina Abdullahi daga Ma’aikatar ayyukan jin kai zuwa ma’aikatar mata, sai Hon. Nasiru Sule Garo, daga ma’aikatar muhalli zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman.
Sai Kwamishinan Kula da Ayyuka Hon. Ibrahim Namadi ya koma ma’aikatar sufuri, yayin da Hon. Umar Haruna Doguwa na ma’aikatar ilimi ya koma ma’aikatar albarkatun ruwa.
Sai kuma Hon. Ali Haruna Makoda an mayar da shi Ma’aikatar Ilimi, Hon. Aisha Lawal Saji daga ma’aikatar mata, yara da nakasassu zuwa Ma’aikatar yawon bude ido da al’adu, da Hon. Muhammad Diggol daga sufuri zuwa ma’aikatar kula da aiyuka.
Gwamnan Kano ya cire Baffa Bichi, Sagagi da wasu Kwamishinoninsa
Wadanda aka bar su a mukaminsu sun hadar kwamishinan shari’a, Barr. Haruna Isa Dederi, Kwamishinan Noma, Dr. Danjuma Mahmoud, Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran, kwamishinan kasa da tsare-tsare, Hon. Abduljabbar Mohammed Umar, kwamishinan kasafi da tsare-tsare Hon Musa Suleiman Shannon da kwamishinan ayyuka da gidaje Engr. Marwan Ahmad.
Sauran su ne kwamishinan albarkatun kasa da ma’adinai, Sefiyanu Hamza, kwamishinan harkokin addini, Sheikh Ahmad Tijani Auwal, kwamishinan matasa da wasanni, Hon. Mustapha Rabiu Kwankwaso, Kwamishinan Kasuwanci, Adamu Aliyu Kibiya da na Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman, Manjo Janar Mohammad Inuwa Idris Rtd.
Sanarwar ta ce gwamantin ya cire Sakataren gwamnatin jihar kano Abdullahi Baffa Bichi Saboda Rashin lafiya, Sannan kuma ya rushe Ofishin shugaban ma’aikatansa Shehu wada Sagagi.
Kwamishinonin da aka sauke sun hadar da Baba Halilu Dantiye na yada labarai da Kwamishinan Kuɗi Ibrahim Jibril Fagge da Shehu Aliyu Yammedi kwamishinan aiyukan na musamman sai kuma Abbas Sani Abbas na ma’aikatar raya karkara da Ladidi Ibrahim Garko kwamishiniyar al’adu da yawon bude ido.