Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi garanbawul a majalisar zartarwarsa .
Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa kadaura24 ranar alhamis.
Sanarwar ta ce gwamanan ya cire Sakataren gwamnatin jihar kano Abdullahi Baffa Bichi Saboda Rashin lafiya, Sannan kuma ya rushe Ofishin shugaban ma’aikatansa Shehu wada Sagagi.
Kwamishinonin da aka sauke sun hadar da Baba Halilu Dantiye na yada labarai da Kwamishinan Kuɗi Ibrahim Jibril Fagge da Shehu Aliyu Yammedi kwamishinan aiyukan na musamman sai kuma Abbas Sani Abbas na ma’aikatar raya karkara da Ladidi Ibrahim Garko kwamishiniyar al’adu da yawon bude ido.
Karin bayani na nan tafe