Daga Rahama Umar Kwaru
Falakin Shinkafi Amb Yunusa Yusuf Hamza, ya yi kira ga iyaye da su cigaba da barin ya’yansu mata su nemi ilimin aikin jarida duba da muhimmacin da yake da shi ga al’umma.
” Babu shakka aikin jarida yana bukatar mata a cikinsa saboda aiki ne na tausayawa al’umma kuma kowa ya san yadda mata suke da tausayi, don haka idan suka sami damar aikin jarida za su iya taimakawa fiye da yadda Maza suke yi”.
Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne yayin wata gasar karanta labarai da hukumar kula da manyan makarantun sakandiren ta jihar kano ta shiyawa makarantun mata a Kano mai taken “Feature News Casters”.

Ya ce muddin iyaye da malaman da suke koyar da aikin Jarida suka kara kaimi a nan gaba za a sami kwararrun yan jarida mata wadanda za su hidimtawa al’ummarsu fiye da yadda ake tsammani.
” Na ji dadi sosai da yadda na ga ni kuma na ji yaran nan suna karanto labarai, kuma ba dan ba danba da sai na ce ai ko masu karanta labaran a gidajen radio ba su fisu iya wa ba, tabbas hakan ya nuna cewa nan gaba kadan za a kara samun kwararrun yan jarida mata a jihar kano”. Inji Falakin Shinkafi
Sarki Sanusi II ya Magantu Kan Hana shi zuwa Bichi da jami’an tsaro suka yi
Amb. Yunusa Yusuf Hamza wanda shi ne ya dauki nauyin shirya gasar ya bukaci iyaye da malamai a jihar kano da su kara karfafa gwiwar dalibai mata domin samun nagartattun yan jarida nan.
Ya ce dole ne iyaye su ƙarfafawa iyayen su gwiwa tare da barinsu su koyi abun da suke so a ransu , wanda hakan zai da yaran su cimma burikansu na rayuwa.
Daliba Fatima Musa Garba daga makarantar yan mata ta kofar kudu dake gidan sarkin Kano ce ta sami nasarar lashe gasar.