Kungiyar kanikawan mota ta ƙasa reshen jihar kano wato NATA, ta cire tallafin man fetur da shugaban ƙasa ya yi yayi kassara ‘yayan kungiyar da dama .
Kadaura24 ta rawaito Shugaban NATA na Kano Yahya Ibrahim ne ya Bayyana hakan yayin wata ziyarar da suka kai wa shugaban karamar hukumar Rano Muhammad Yau, kamar yadda Jami’in yada labaran shiyyar Rabi’u Kura ya fitar ga manema labarai.

Ibrahim ya bayyana tsananin talauci da kanikawa su ke fuskanta sakamakon wancan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka
Sanarwar ta bayyana cewa, “kaso 40 cikin 100 na kanikawa a Kano yanzu sun bar sana’ar saboda cire tallafin man fetur, lamarin da ya jawo koma mutane da yawa suka Ajiye ababen hawansu.
Sanarwar ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta taimakawa kanikawa domin su ci gaba da Sana’ar su.
Ziyarar ta zo dai-dai da shirye-shiryen tunkarar zaben kananan hukumomin NATA da ke tafe.