Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Ali Madakin Gini ya baiyana cewa abin dariya ne a ce waɗanda ba ƴan jam’iyyar NNPP ba su yi yunƙurin cire shi daga muƙamin sa.
A wata tattaunawa da jaridar DAILY NIGERIAN, Madaki ya zargi jagoran NNPP na ƙasa, Rabi’u Kwankwaso da kitsa yunƙurin tsige shi daga muƙaminsa.
A cewar sa, ya za a yi waɗanda shugabancin jam’iyya na ƙasa ya kore su, kuma su sami ikon cire wani daga muƙamin sa, inda ya ƙara da cewa wani yunkuri ne na wasu da su ke rawa da bazar Kwankwaso “kuma su ke ganin cewa duk abinda ya faɗa ta zauna.”

“Waɗanda su ka rattaba hannu a takardar ba yan jam’iyyar NNPP ba ne. Kwanan nan kotu ta kori shugabancin jam’iyar bangaren Kwankwaso.
“Saboda haka wannan su na bata wa kan su lokaci ne kawai saboda kwanan nan kotu to kori shi kansa Kwankwason daga jam’iyyar. Amma ka san dole su rika rawa da bazar Kwankwaso,” in ji Madaki.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito wasu yan majalisar tarayya na jam’iyyar NNPP 15 daga cikin 18 sun nemi a tsige Madakin gini daga muƙaminsa na mataimakin shugaban marasa rinjaye.