Dalilin da yasa aka sauke Sarki Sanusi II daga Khalifancin Tijjaniyya a Najeriya – Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Rahotanni na cewa Shugaban ƙungiyar Tijjaniyya na Afrika, Sheikh Mahy Sheikh Ibrahim Inyass, ya sanar da tsige Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II daga matsayin Khalifan Tijjaniyya a Najeriya.

Wannan sanarwa na ƙunshe ne cikin wata takarda wacce aka rubuta kuma aka aikewa manema labarai da sauran mambobin darikar Tijjaniyya da ke faɗin Najeriya a ranar Talata 26th ga watan Nuwambar, 2024.

Takardar mai ɗauke da sa hannu da Stampin shugaban ƙungiyar Tijjaniyya na Afrika, Sheikh Mahy Sheikh Ibrahim Inyass, ta ce daga yau ta Cire Muhammadu Sanusi II daga Khalifancin Tijjaniyya kuma ta soke ofishin Khalifancin Tijjaniyya a Najeriya.

Talla

Da yake yiwa Kadaura24 karin bayani mai magana da yawun Sheikh Mahy Sheikh Ibrahim Inyass wato Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi yace Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Al-Husain ne za su cigaba da gudanar da duk wasu harkokin darikar Tijjaniyya dake faɗin Najeriya .

“Da ma a darikar Tijjaniyya ba a baiwa sarki khalifanci, ko a baya ma an baiwa Sarki Sanusi na 1 khalifancin Tijjaniyya ne bayan da aka sauke shi daga sarkin Kano, haka shi ma Muhammadu Sanusi II sai da aka sauke shi sanann aka ba shi, saboda kar ya shiga damuwa”. Inji Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi

Madakin Gini ya yiwa Kwankwaso martani kan batun tsige shi daga muƙaminsa na majalisa

“Tun a baya Sheikh Mahy Inyass ya so ya karbe khalifancin na Muhammadu Sanusi II, amma sai aka ba shi shawarar idan aka sauke shi zai ji cewa an wulakanta shi, shi yasa aka bar shi, amma yanzu tunda ya ce ya dawo sarautar Kano to shi yasa aka cire shi tunda ya zabi Sarauta fiye da khalifancin Tijjaniyya”.

Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya bukaci dukkanin yan darikar Tijjaniyya da su Kasance masu biyayya ga wannan umarni domin samar da masalaha a darikar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...