Kamfanin mai na Nigeria ya bayyana cewa matatar mai ta garin Fatakwal da ke Jihar Rivers ta fara aikin sarrafa mai.
Wannan bayani ya fito daga bakin Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL), Femi Soneye.

“A yau an samu gagarumin nasara ga Najeriya yayin da Matatar Fetur ta Port Harcourt ta fara sarrafa mai a hukumance. Wannan matakin ya ƙaddamar da sabon babi na cin gashin kai a fannin makamashi da haɓaka tattalin arziki a ƙasarmu,” in ji Soneye a ranar Talata.
“Muna taya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Hukumar Gudanarwa ta NNPC, da kuma jagorancin Mele Kyari murna bisa irin namijin ƙoƙarinsu a wannan aikin juyin juya hali. Tare, muna canza makomar makamashin Najeriya!”.
Madakin Gini ya yiwa Kwankwaso martani kan batun tsige shi daga muƙaminsa na majalisa
Soneye ya kuma bayyana cewa za a fara lodin man fetur a cikin motocin daukar kaya a ranar Talata (yau), tare da ƙara da cewa NNPCL tana kuma yin aiki tukuru don dawo da Matatar Fetur ta Warri nan ba da jimawa ba.