Khalifan Tijjaniyya na duniya Sheikh Ibrahim Mahy Inyass ya musanta batun sauke Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II daga khalifancin Tijjaniyya na Nigeria.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa guda cikin masu magana da yawun Khalifa Sheikh Mahy wato Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya bayyanawa kadaura24 cewa an sauke sarkin Sanusi II daga khalifancin Tijjaniyya saboda ya dawo gadon sarautar Kano.

A wata ganawa da Manema labarai a Kano guda cikin masu magana da yawun Khalifa Sheikh Mahy wato Sheikh Sani Auwalu Ahmad ya ce batun da Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya yi na sauke sarki Sanusi II ba shi da tushe ballantana makama.
” Jawabin da Alhaji Ibrahim Dahiru Bauchi ya yi ba shi da wata madogara, duk da shi ma yana daga cikin masu magana da yawun Shehi Mahy, maganar ba gaskiya ba ce kawai yana son ya hada husuma ne, da kuma kokarin nemawa kansa suna”.
Ya bukaci al’ummar Nigeriya da duk mabiya darikar Tijjaniyya da su yi watsi da waccen maganar ta sa, domin ba ta da wani tushe kuma ba da yawun Shehi Mahy ya yi ta ba.