Yan Arewa ne suke kalubalantar kudirin haraji na Tinubu, Amma za a wayar musu da kai – Abdulmumini Kofa

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da gidaje da muhalli Hon Abdulmumin Jibrin ya ce majalisar za ta tabbatar da kudirin sauya fasalin haraji da Tinubu ya aika musu ya zama doka ba nan ba da jimawa ba.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a cikin wani shiri mai suna Politics Today a gidan Talabijin na TVC ranar Lahadi.

Abdulmumini Jibrin ya ce sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ke yi a halin yanzu zasu zamo abun alfahari ga Nigeriya nan gaba, inda ya kara da cewa majalisar dokokin kasar za ta yi nazari kan kudirorin kuma idan zai yiwu, ta gyara abubuwan da ake cece-kuce kafin a amince da su.

Talla

Ya ce, “Ban taba samun wani shakku ba game da amincewa da kudirin gyaran haraji. Za mu tabbatar da kudirin ya zama doka”.

Ya kara da cewa, yan Arewacin Nigeria ne suke sukar kudirin sauya fasalin haraji da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatarwa majalisar, amma ya ce akwai bukatar a wayar da kan ‘yan Najeriya kan cancanta da kuma wajabcin gyara fasalin haraji.

Labari mai dadi: Dangote ya rage farashin litar man fetur dinsa

“Mu da muka karanta daftarin kudirin, Mun fahimci alfanunsa ya fi yawa sosai fiye da illarsa mutane suke zato”. Inji Kofa

Eh, mai yiyuwa ne za a iya samun wasu kura-kurai da ke jawo cece-kuce a cikin kudirorin, amma saboda hakan bai kamata a ce a yi watsi da shi ba ko kuma Majalisar Dokoki ta kasa ta ki amincewa da shi ba”.

Abdulmumini Kofa ya ce tunda kudurin dokar yanzu haka yana wajensu to akwai bukatar a basu dama su gudanar da aikinsu na yan majalisa akan kudirin ta yadda zasu gyara duk wani abu da yake haifar da ce-ce-ku-ce akan kudirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...