Daga Abubakar Lawan Bichi
Kungiyar Tsofafin na daliban Kwalejin horas da malaman Kimiya da Fasaha ta Gwamnatin Tarrayya dake Bichi wato Federal College of Education (Technical) Bichi. (Alumni) a karan Farko ta gudanar da zaben Shugabanninta wanda ya gudana a Babban dakin taro na Kwaleji a tsohon mazaguni dake Bichi.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban Kwamitin zaben Ambasada Ibrahim Bala Aboki shi ne wanda ya jagoranci gudanar zaben, wanda aka sami yan takarar Shugabanci Kungiyar guda biyu, Hon Mahmoud Sani Madakin Gini da Kuma Shelk Mukhtar Tafida.

Da yake bayana sakamakon zabe jami’im zaben Ambasada Ibrahim Bala Aboki, ya bayyana Hon Mahmoud Sani Madakin Gini a matsayin wanda ya yi Nasara da kuri’u 263, sai abokin takararsa Shelk Tafida Mukhtar da ya sami kuri’u 139.
Amb. Aboki ya ce Mahmoud Madakin Gini shi ne ya sami kuri’u masu yawa don haka shi ne ya lashe zaɓen shugaban kungiyar.
Ga jerin sunayen sauran wadanda za su jagoranci kungiyar.
Dagacin da ya Shekara 91 yana mulki ya Rasu
Victoria Owolabi a matsayi mataimakin Shugaban, Oluwatosin Owolabi a Matsayi Magatakadar Kungiyar, Aliyu Ibrahim Bichi ma’aji, Kabiru Bala Mataimakin Magatakadar, Nafisa Shehu Abubakar Sakatariyar Kudi, Ibrahim Musa Ibrahim Sakatare yada Labarai, Ambali A Aderemi Mai bincike Kudi, Ibrahim Dodo Muhammad Jami’am jin dadi na kungiyar, Ado Muhammad Kachako jami’im mai kula da Ajujuwa na Shekara 1991 zuwa 1996. da kuma ajujuwa na 1997 zuwa 2002.
Ambasadar Aboki ya godewa dukkani wanda suka bayar da gudunmawa kafin zaben, lokacin da zaben da kuma bayan zaɓen.
A Jawabinsa Sabon Shugaban Kungiyar Hon Mahmoud Sani Madakin Gini ya yi alkawarin yin aiki tukura don ciyar da Kungiyar gaba da hada kai dukkani yan Kungiyar domin samar musu da cigaba.