Zaɓen Kananan hukumomi: Gwamnatin Kano ta nemi a sauya alƙalin da zai yi Shari’ar

Date:

Gwamnatin Jihar Kano ta zargi mai shari’a Simon Amobeda na Babbar Kotun Tarayya dake jihar da nuna son zuciya a shari’ar zaben kananan hukumomi da aka gabatar a gabansa.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito jam’iyyar APC ce dai tare da wasu masu ruwa da tsaki su ka shigar da kara su na neman kotu ta bayyana cewa ba a samu zababbun shugabannin kananan hukumomi ba a jihar Kano.

Talla

Jaridar GUARDIAN ta rawaito cewa a zaman fara sauraren korafe-korafen da aka shigar a jiya Juma’a, Antoni Janar na Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Isa Haruna Dederi, ya nemi Mai Shari’a Amobeda ya janye kansa daga shari’ar saboda zargin nuna son zuciya da ya ce alkalin ya yi a lokuta da dama a kan gwamnatin Kano.

A cikin takardar da ya gabatar, Dederi ya yi zargin cewa mai shari’ar yana da wata kiyaiya a zuciyarsa da ya nuna ga gwamnatin jihar da hukumominta tun bayan da aka shigar da wani korafi ga Hukumar Kula da Alkalai ta Kasa (NJC) da ke zarginsa da cin gajiyar iko da kuma bayar da umarni ba bisa ka’ida ba.

Inganta tsoro: Kwamishinonin mata a Arewacin Nigeria sun gudanar da taro na musamman

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta lura da “wadansu abubuwan da ba su dace ba” musamman game da shari’o’in da suka shafi mutanen da ke da alaka da siyasa, musamman wadanda ke cikin jam’iyyun adawa, da aka gabatar gabansa. Wannan, a cewar gwamnatin, yana nuna wata alaka tsakanin mai shari’ar da wata jam’iyyar adawa.

Gwamnati ta kuma ce “Mai shari’ar ya sha fitowa a jaridu yana barazanar fallasa wani jami’in gwamnatin Jihar Kano da ya rubuta karar a kansa, yana nuna fushinsa tare da kokarin tabbatar da cewa karar ba ta dace ba.”

Duk da haka, Mai shari’a Amobeda, yayin nuna rashin amincewa da bukatar da gwamnatin ta gabatar na ya janye kansa daga shari’ar, ya ce ba ya goyon bayan wani bangare kamar yadda ake zarginsa, sai dai yana goyon bayan adalci ne kawai.

Mai shari’ar, yana martani, ya ce, “Lauyoyi marasa kwazo ne kawai ke gabatar da bukatar alkali ya janye kansa daga shari’a,” sannan ya zargi lauyoyin Jihar Kano da yin “abubuwa marasa kyau” a kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...