Ƙanin Kwankwaso ya maka Gwamna Abba Gida-Gida a Kotu akan Batun Fili

Date:

 

Garba Musa Kwankwaso, ƙanin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya shigar da kara a gaban kotu domin ta hana gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar daukar wani mataki a kan wani fili.

A cikin karar har da hukumar KNUPDA da Kwamishinan Shari’a na jiha da sauran wasu mutane.

DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa asalin filin Kwankwaso ne ya baiwa wani kamfani mai suna WAECO, amma sai gwamna Abdullahi Ganduje ya kwace filin.

Talla

Daga baya sai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta tabbatar da kwace filin, wanda ya ke a rukunin gidaje na Kwankwasiyya City, bisa hujjar cewa lokacin da su ka bada filin ga Kamfanin WAECO bai yi rijistar zama cikakken kamfani ba.

Daga nan ne sai Ganduje ya dawo da kasuwar yan magani cikin wani bangare na filin.

Zaɓen Kananan hukumomi: Gwamnatin Kano ta nemi a sauya alƙalin da zai yi Shari’ar

Shi ma Abba da ya hau, sai ya ƙi maidawa kamfanin WAECO filin, shi ne Garba Kwankwaso ya shigar da kara.

A umarnin da ya bayar, Mai Shari’a Usman Na’abba ya bada umarnin hana taba filin ga gwamnati, sannan ya dage sauraren koken zuwa 27 ga watan Nuwamba.

Daily Nigerian

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...