Yawan ciyo bashi: Atiku ya gargaɗi Tinubu

Date:

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya ce yawaitar ciyo basussuka da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ke yi zai ƙara jefa tattalin arzikin Najeriya cikin ƙunci.

Tsohon ɗantakarar na PDP ya kuma soki yadda majalisar dokoki ke amincewa da buƙatar ciyo basussukan, waɗanda a cewarsa suke ƙara jefa ƙasar cikin ƙangin bashi.

Talla

Atiku ya bayyana haka ne a wani rubuta da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce, “rahoton da bankin duniya ya fitar kwanan nan, wanda ke nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta uku da ta fi cin bashi daga hukumomin kuɗi na duniya abin damuwa ne.

“Rahoton ya fito ne a daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ta aike da wata buƙatar sake ciyo wani bashin na naira triliyan 1.7 saboda cike giɓin kasafin kuɗin 2024. Abin da zai ƙara ɗaga hankali a game da bashin ma shi ne kasancewarar a kasafin kuɗin, an kasafta darajar dala ɗaya a kan naira 800, alhali yanzu dala ta kai naira 1,600.”

Kwamitin amintattun KCSF ba shi da hurumin dakatar da ni – Ibrahim Waiya

Ya ƙara da cewa Najeriya na ƙara nutsewa a cikin bashi, “sannan majalisar dokoki suna taimakawa. Tinubu ya bayyana a watan Yuli cewa hukumar tattara haraji da kwastam sun tara kuɗin shiga da ba a taɓa tarawa ba. To me ya sa ake cin bashin? akwai wani abu da suke ɓoyewa ƴan Najeriya.”

Atiku ya ƙara da cewa yawan cin bashin yana ƙara takurawa tattalin arzikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...