Shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula da ke jihar kano Amb. Ibrahim Waiya ya ce har yanzu shi ne halastaccen shugaban gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu na jihar Kano.
“Wannan sanarwar data fita mai ɗauke da sa hannun sakataren kwamitin amintattu su sani cewa a dokance basu da hurumi na tsige mamba a ƙungiya balle shugaba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Amb. Waiya kan harkokin yada labarai Bashir A Bashir ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Ya kara da cewa “Muna tabbatar da cewa masu shirin tada wannan tarzoma ba don komai suke ba, sai don wani kuɗiri na ƙashin kansu, wanda ba cigaba ne ga al’ummar jihar Kano ba.
Zanga-zangar yunwa: Gwamnan Kano ya baiwa mutane biyu aiki cikin matasa 76 da aka mikasu ga iyayensu
“A saboda haka muna kira ga mambobin gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu na jihar Kano da suyi fatali da wannan sanarwar tare da jiran me kotu zata faɗa a mako mai zuwa”. Inji sanarwa
Sanarwar ta ce Ibrahim Waiya yana ƙara haƙurƙuntar da mambobin KCSF musamman masu kishin jihar Kano na tabbatar da samun Nasara a gaban kotu.