Zanga-zangar yunwa: Gwamnan Kano ya baiwa mutane biyu aiki cikin matasa 76 da aka mikasu ga iyayensu

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya mika yaran Kano 76 da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sallame su bisa laifin cin amanar kasa ga iyayensu.

Biyu daga cikinsu an yi musu alkawarin ba su aikin gwamnati nan take Sannan kuma za a mayar da sauran makarantu.

Yaran da ‘yan sanda suka kama yayin zanga-zangar yunwa a jihar Kano a ranar 1 ga watan Agusta, sun sha fama da yunwa da wahalhalu na tsawon watanni uku a hannun ‘yan sanda a Abuja.

Talla

Bayan korafe-korafe shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin sakinsu, hakan tasa Gwamna Yusuf yasa aka kwantar da su a asibitin kwararru na Muhammadu Buhari domin ba su kulawa ta musamman.

Yayin da yake mika yaran ga iyayensu a ranar Alhamis, Gwamna Yusuf ya yaba wa shugaba Tinubu bisa Afuwar da ya yi wa yaran, wanda hakan yasa aka sallame su daga kotun .

Yanzu-yanzu: Majalisar Wakilai ta ki amincewa da kudirin neman karawa shugaban kasa wa’adi

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 yace gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan sa Alh. Shehu Wada Sagagi, Gwamnan wanda ya nuna damuwarsa bisa barnatar da kadarori na biliyoyin nairori a lokacin zanga-zangar .

Don haka ya ja kunnen matasa da su zama ’yan kasa na gari masu kishin Nigeriya kuma su zamo jakadun Kano na gari ta yadda za a yi alfahari da su.

Tun da farko kwamishinan ilimi na jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa ya bayyana cewa gidauniyar Bafarawa ta baiwa dukkanin yara su 76 tallafin kudi N50,000 ga kowannesu. Doguwa ya ce ma’aikatarsa za ta fara mayar da yaran makaranta cikin gaggawa kamar yadda gwamna ya umarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...