Majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin dokar da ke neman mayar da wa’adin shugabancin Najeriya ya koma shekaru shida, amma falle daya.
An yi watsi da kudirin dokar, wanda ake shirin yiwa karatu na biyu a yayin zaman taron na ranar Alhamis.
Kudirin dokar dai da ya wuce zai sauya tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Nigeriya, na samar da waβadin mulki na shekaru shida ga shugaban kasa da gwamnonin jihohi.

Hon. Ikenga Ugochinyere ne ya gabatar da kudirin , Wanda ya bukaci wa’adin mulkin Shugaban kasa da gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi ya koma falle daya amma ya kai shekaru shida .
Kudirin ya kuma nemi a ba da damar gudanar da dukkan zabukan shugaban kasa, gwamna da yan majalisu duk a rana daya.
Da dumi-dumi: Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya ciyo bashin $2.2bn
A lokacin da aka kada kuri’a a kan kudirin dokar da aka shirya yi wa karatu na biyu, yawancin ‘yan majalisar sun kada kuri’ar kin amincewa da shi.
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya kadaura24 ta rawaito tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayar da shawarar a gyara kundin tsarin mulkin kasar na 1999 da dokar zabe ta 2022, saboda a bada dama wa’adin shugaban kasa ya koma na tsawon shekaru shida, sannan a rika baiwa kowacce shiyya dama .