Gwamnatin jihar Neja ta ce za ta gabatar da rahoto ga jami’an tsaro domin su ci gaba da bincike kan wani malamin addini musulunci da ta dakatar bayan zargin sa da yaɗa ‘aƙidar Boko Haram’.
Shugaban Hukumar lura da al’amuran addinai ta jihar Neja, Umar Faruk ya shaida wa BBC cewa an dakatar da malamin ne bayan binciken da gwamnatin jihar Neja ta yi a kansa.
Ya ce “kwamitin da muka kafa ya kira shi kuma mun tattauna da shi, mun gano cewa bai ma yi karatu ba.”

A cewar sa malamin na gudanar da ayyukansa a garin Tafa da ke jihar Neja, inda ya mallaki Islamiyya kuma yana da mabiya wadanda ke halartar darussansa.
“Da muka lura cewa tafiyarsa da aƙidarsa da da’awarsa akwai hatsari ga tsaron jihar Neja da tsaron kasa, shi ne muka yanke hukuncin cewa a dakatar da shi kuma a rufe makarantarsa har sai jami’an tsaro sun yi bincike a kansa,” in ji Sheikh Faruk.
Ya ƙara da cewa malamin yana kira ne ga magoya bayan sa da su ƙaurace wa zaɓuka da duk wani abin da ya shafi dimokuraɗiyya.
Najeriya dai ta kwashe sama da shekara 10 tana fama da matsalar mayaƙan Boko Haram waɗanda suka addabi arewa maso gabashin Najeriya da kuma wasu ƙasashen yammacin nahiyar Afirka.
Haka nan ƙasar na fama da matsaloli na ƴan fashin daji masu garkuwa da kisan mutane a arewa maso yammacin ƙasar.
Dama dai malamin ya riƙa janyo cece-ku-ce a yankin arewacin Najeriya sanadiyyar kalaman da ya riƙa furtawa kan malaman addinin Musulunci da dama na yankin.