Daga Aminu Yahaya Tudun Wada
Wata gobara da ta tashi ranar alhamis a layin yan katago dake kasuwar Gama Bridgate a karamar hukumar Nasarawa jihar kano ta yi asarar duban nairori.
Rahotanni sun nuna cewa akalla anyi asarar sama da naira million dari sanadiyar gobarar data tashi.
Gobarar ta tashi da misalin karfe 1:05am na daren jiya laraba, amma ba a samu asarar rai ko daya ba, amma ta kone dukiya da runfuna kusan bakwai.

Shugaban kasuwar Mal Abdullahi Usaini Babandi ya bayyana cewa musabbabin tashin gobarar daga Allah ne amma basa tunanin akwai sakaci wajen tashin gobarar. Sannan ya yabawa jami’ an kashe gobara ta jihar kano, tare da kira ga Gwamnatin jihar Kano data tallafa musu.
Shi ma Malam Muhammdu Saminu Yakubu na guda daga cikin wadanda runfarsu ta kone kurmus ya bayyana cewa katsam cikin dare aka kirashi da cewa Gobara ta tashi a runfarsa wanda tayi sanadiyar kone duk wasu kayyaki dake runfar tasa, kuma shima dai ya yabawa Yan kwana-kwana bisa kokarin da su ka yi tare da neman daukin Gwamnati da masu hannu da shuni.
Lugudan Wuta da sojojin Nigeria ke yi ya tilastawa Lakurawa tserewa daga jihohin Kebbi da Sakkwato
Hukumar kashe gobara ta jahar Kano, karkashin jagorancin babban Daraktan ta, Alhaji Hassan Ahmed Muhd, ta karbi kiran gaggawa daga wani jami’in dan sanda mai suna ASP U.I. Bushira , dake aiki a ofishin yan sanda na Dakata, inda ya sanar da su iftila’in tashin Gobara a kasuwar Brigade Yan Katako, da misalin karfe 1:51am na daren jiya Laraba 13 ga watan Nuwamban 2024.
Kakakin hukumar kashe gobara na jahar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce bayan zuwan jami’an hukumar kashe gobarar sun tarar da wasu shaguna guda biyu wadanda suka kama da wuta, har suka samu nasarar shawo kan lamarin.
Sai dai wutar ta sake tashi a wasu shagunan guda biyu, a wajen da wutar ta fara tashi da farko , kuma jami’an sun yi kokarin tsayar da wutar a iya shaguna hudu da suka tabu ba tare da ta ci gaba da yaduwa zuwa sauran shagunan ba.
Saminu Yusuf ya kara da cewa , gobarar ta tashi ne sakamakon dawo da wutar lantarki, kuma akwai wata na’urar wutar lantarki da ba a kashe ba, wanda shi ne musabbabin tashin wutar.