Dalilin da ya sa APC ke son a hana ƙananan hukumomin Kano kuɗin wata-wata

Date:

 

A jihar Kano dai ana ci gaba da zaman doya da manja tsakanin APC da NNPP inda kowannensu ke ƙoƙarin ganin ya shiga gaba a harkokin siyasar jihar mai yawan al’umma a arewacin Najeriya.

Dambarwar baya-bayan nan dai ta faru ne bayan da jam’iyyar APC a jihar ta Kano ta nemi kotu ta dakatar da hukumomin gwamnatin tarayya daga bai wa ƙananan hukumomin jihar kason kuɗinsu na wata-wata.

Wannan na zuwa ne bayan da wata kotu ta bayar da umarnin hana duk wata hukuma ko wani yunƙurin dakatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar.

Tun kafin zaɓen ƙananan hukumomin jihar dai ake ta kai ruwa rana tsakanin APC da NNPP wanda har kotu ta bayar da umarnin ka da a gudanar da zaɓen amma daga bisani wata babbar kotun jiha ta bada umarnin a yi zaɓen.

Talla

Hujjojin da APC ta gabatar wa kotu

Jam’iyyar APC a Kano da kuma shugabanta Abdullahi Abbas tare da wani mai suna Aminu Aliyu Tiga sun garzaya gaban babbar kotun tarayyar suna neman kotun ta hana bai wa ƙananan hukumomin jihar 44 kuɗaɗensu bisa dalilan cewa shugabannin ƙananan hukumomin da aka zaɓa haramtattu ne.

“Akwai hukuncin da wata kotu ta bayar cewar hukumar zaɓe ta Kano ba ta cancanci ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi ba saboda kusan duk shugabannin hukumar na da alaƙa da jam’iyyar NNPP kenan jami’an na cikin siyasa dumu-dumu.

To amma suka yi zaɓen duk da wancan hukuncin na kotun saboda haka ne masu ƙara suka ga rashin halartar shugabannin ƙananan hukumomi shi ya sa suka shigar da ƙara da a dakatar da bai wa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu na wata-wata har sai an gudanar da sahihin zaɓe.” In ji Barista Nura Adamu Isa ɗaya daga cikin lauyoyin masu ƙara dangane da hujjojin da suka bayyana wa kotun.

Gwamantin Kano za ta fara Kama Yaran da suke yawo a titunan birnin

Kotun dai ta bayar da umarnin gabatar da takardun ƙara ga ɓangarori 56 ciki har da ministan shari’a da kuma kwamishinan shari’a na Kano wanda shi kuma zai mika wa ƙananan hukumomin jihar Kano 44 takardun.

Hukuncin wata kotun
To a gefe guda dai, tun kafin wannan ƙara da APC ta shigar, wasu ma’aikatan ƙananan hukumomi a Kano da wasu ‘yan gwagwarmaya sun shigar da ƙara a a wata babbar kotun jihar, inda kuma suka samu umarnin kotun na dakatar da duk wani yunƙuri daga kowanne ɓangare ko hukuma, na hana ƙananan hukumomin kuɗaɗensu.

“Sun nemi mu shigar da ƙara a gaban kotu domin bada umarni ga babban bankin Najeriya da babban akantan Najeriya da hukumar da ke rarraba kuɗaɗen ƙasa da ka da su taɓa ko yin wani abu da zai haifar da tsaiko ga bai wa ƙananan hukumomin Kano kuɗaɗensu na wata-wata.” In ji Barista Bashir Tudun Wuzirci wanda shi ne lauyan masu ƙara.

Babbar kotun tarayyar dai ta ɗage sauraron wannan ƙara zuwa ranar 22 ga wannan wata na Nuwamba, domin sauraron dukkan ɓangarorin.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...