Daga Umar Hamza Gwangwazo
Na samu labarin wasu wadanda aka dauki nauyinsu, suka fake da sunan kungiyar “Renewed Hope Ambassadors Forum” suna zargin tsohon ministan gidaje da raya birane Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo da sukar shugaban kasa a kafafen yada labarai, wai saboda an cire shi daga mukamin minista.
Da farko, bincike ya nuna cewa makaryata ne an dauke su a matsayin karnukan farauta. Wannan ya tabbatar da cewa kungiya ce da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin ya samar domin yiwa jam’iyyar APC zagon kasa a Kano. Sakamakon wannan kungiya bata da rijista don haka ba wani akilin mutum da zai yarda da maganganun da suka yi akan tsohon Ministan ba.
Sabanin ikirarin waccan kungiyar, tsohon Ministan bai fito fili ya fadawa Shugaban kasa wata magana mara dadi ba, hasalima hakan ba halinsa ba ne kuma bai yi dai-dai da tsarin siyasarsa ba.
Tsohon Ministan dai mai biyayya ne ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a wata hira da ya yi da BBC Hausa ya ce bai nema ba, shugaban kasar ya zabo shi domin ya yi aiki da shi a matsayin minista don haka bai ga laifinsa ba a lokacin da ya sauke shi daga mukamin Minista, kuma ya godewa shugaban kasar bisa damar da ya ba shi na yiwa al’ummar Nigeriya hidima a gwamnatinsa.

Daya daga cikin dalilan da aka bayar na cire shi shi ne yadda aka tare mukamai a yankin Kano ta Arewa don haka akwai bukatar a nada wani daga Kano ta tsakiya, shi ne Gwarzo ya nuna shakku kan matakin nada Ata, inda ya ce maimakon haka a nada Nasiru Yusuf Gawuna mana tunda shi ne ya yiwa jam’iyyar APC takarar gwamna a 2023.
Idan za a yiwa Gwarzo adalci, ya yi gaskiya da ya ba da wannan shawarar duba da irin abubuwan da suka faru a baya, Gawuna ya fi Ata cancanta idan akai la’akari da nauyinsu a siyasance, kowa ya san cewa a 2023 Ata bai iya kawo ko da mazabarsa ba ballantana karamar hukumarsa ko sanatoriyarsa, kuma a bayyane yake yadda ya yiwa jam’iyyarsa zagon kasa tun lokacin da Aminu Sulaiman Goro ya kada shi a zaɓen fidda gwani na dan majalisar tarayya na karamar hukumar fagge.
T Gwarzo bai zargi Shugaba Kasa Tinubu ba , Kuma har yanzu Gwarzo mai biyayya ne ga tsarin siyasar Shugaba Tinubu don haka ta yaya ma zai suke ubangidansa wanda ya yi masa rana a siyasa?
Har ya zuwa yanzu, Gwarzo ya na ganin kima da mutuncin Shugaban kasa, yana mai kara jaddada biyayyarsa, ba tare da la’akari da halin da ake ciki ba.
APC Kano: Martani, Budaddiyar Wasika Zuwa ga Shugaba Tinubu – Daga Maikudi Lawan
Hatta wadanda suka yi kitsa cire shi sun san cewa Gwarzo shi ne na gaba-gaba wajen yin biyayya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sai kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje.
Ba makawa Abdullahi T- Gwarzo yana cikin manya-manyan masu biyayya ga Shugaban Kasa guda biyar a daukacin Arewacin Najeriya, wadanda suka hadar da su Malam Nuhu Ribadu, Ibrahim Masari, da Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Da alama ikirarin biyayyar da Sanata Barau Jibrin yake yi wa Shugaban kasa iya baki ne kawai, domin tarihinsa dan siyasa ne mai son kansa, wanda yafi fifita bukatar Kansa akan ta al’umma. Tarihi ya nuna Barau yana amfani da mutane ne ya watsar da su idan bukatarsa ta biya.
Ya kamata shugaban kasa ya yi taka-tsan-tsan wajen mu’amala da Sanata Barau Jibrin, duba da tarihinsa na cin amanar wadanda suka taimaka masa ya hau mulki tun 1999. Yanzu haka yana kokarin yin amfani da ofishinsa wajen yaudarar Shugaban kasa da cewa yana da cikakken iko kan siyasar Kano kuma yake so Shugaban ƙasar ya aminta da shi.
Wata Jami’a a London ta Baiwa Baffa Babba Danagundi Digirin Girmamawa
Barau ba zai iya kayar da AT Gwarzo a Gwarzo ba, ba zai iya kayar da Murtala a Kabo ba, Abubakar Kabir Bichi a Bichi, Sani Bala a Tsanyawa da Ghary, Hamisu Chidari a Dambatta da Makoda da Tijjani Abdulkadir Jobe a Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado, haka a Bagwai da Shanono ma.
Yana fakewa ne a karkashin inuwar wadannan mutane domin ya ci zabe, amma ba shi da wani karfi a yankin Kano ta Arewa.
Irin su Sanata Barau suna yi maka biyayya ne kawai idan kana kan mulki. Ya kamata shugaban kasa ya tambayi magabacinsa Muhammadu Buhari game da mutane irinsa.
Umar Hamza Gwangwazo, dan jam’iyyar APC ne ya yi wannan rubutun daga Kano Municipal, Kadaura24 kuma ta fassara.