Daga Abubakar Isa
Tsohon Babban mataimaki na musamman ga tsohon gwamnan jihar kano Alhaji Ado Yellow Mai Tv ya yi kira ga gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya bi a hankali ka da wasu marasa kishin Kano su zuga shi ya cire Kwamishiniyar jin kai Hajiya Amina HOD daga mukaminta.
” Mu yan jam’iyyar APC ne, amma mun gamsu da cewa kwamishiniyar ma’aikatar jin kai Hajiya Amina HOD aikinta ta gudanar a matsayinta ta wacce take kula da jin kan al’umma, don haka bai da ce don mutum yayi Aikinsa ba kuma wasu su zo su yi masa sharri kuma har a yarda da bayansu”.
Alhaji Ado Yellow Mai Tv ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da yayi a Kano.

Ado Yellow wanda shi ne shugaban kungiyar APC integrity group na jihar Kano ya ce bai dace a harkar da ta shafi kiwon lafiyar al’umma a sanya siyasa ba, shi yasa suka ga dacewar tsuma baki akan wannan batu, kasancewar jihar kano ita suke kallo ba wani abu ba.
” Kowa yasan yadda likitoci a Kano suka yi kaurin suna wajen cin zarafin marasa lafiya da sauran al’umma, don haka mu muna ganin ba gaskiya ba ne abun da likitar nan ta fada , saboda mun fahimci kawai so likitocin suke sai sun gamsar da mutane akan karya, to muna so ku sani Mun gano ku”. Inji Ado Yallow
Gwamnan Kano Ka Cire Kwamishiniyar Jin Kai Saboda Za ta Jawo Maka Bakin Jini -Anas Abba Dala
Ya ce kiran da Kungiyar likitocin ta yiwa gwamnan jihar kano na ya cire Kwamishiniyar raini ne, ita kungiyar ai bata Isa ta cewa gwamna ga abun da zai yi ba , sai dai ta kai masa koke shi kuma ya duba ya dauki matakin da ya dace.
” Ina kira ga mai girma gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya bincika ya kuma tabbatar da cewa bai cire Kwamishiniyar ba, saboda aikin da ya dora mata ta yi, kuma idan har wata kungiyar zata yi maka barazana kuma ka bi Abin da take so, to gaskiya za a sa kai ta rabuwa da mutanen kirki a gwamnatinka”. A cewar Ado Yellow mai Tv
Ya ce duk da cewa su yan jam’iyyar APC ne amma sun yarda da nagartar Hajiya Amina HOD, don haka ne ma suka ga dacewar shiga maganar, saboda idan aka ce an cireta daga wannan mukamin to jihar Kano ce zata cutu saboda jajirtacciya ce mai kishin al’umma.
Idan za’a iya tunawa dai kadaura24 ta rawaito cewa an sami rashin jituwa tsakanin kwamishiniyar ma’aikatar jin kai ta jihar kano Hajiya Amina HOD da wata likita a asibitin kwararru na Murtala Muhammad, wanda har ta kai ga kungiyar likitoci da wasu yan siyasa sun fara kira ga gwamnan Kano da ya sauketa daga mukamin kwamishiniya.
Hakan dai ya jawo har sai gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kafa wani kwamiti karkashin jagorancin kwamishinan lafiya na jihar kano domin su binciki lamari tare da gabatar masa da rahoton binciken cikin kwana biyu.