Ku hanzar ta fara aiki a harabar MAAUN dake Gwarzo don inganta Ilimi – T Gwarzo ga Farfesa Adamu Gwarzo

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Tsohon Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane Mai Girma Abdullahi Tijjani Gwarzo ya bukaci mahukuntan Jami’ar Maryam Abacha da su hanzarta tabbatar da kudirinsu na samar da harabar Jami’ar dake garin Gwarzo.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga tsohon Ministan Kan harkokin yada labarai Adamu Abdullahi ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Tsohon Ministan ya yi wannan roko ne a lokacin da ma’aikatan Jami’ar karkashin jagorancin Shugaban Jami’ar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo suka kai masa ziyara a gidansa na Rijiyar Zaki, Kano, domin jajanta masa kan cire shi da aka yi daga mukaminsa.

Talla

T Gwarzo wanda ya nuna jin dadinsa da ziyarar, ya bayyana Farfesa Adamu Gwarzo a matsayin mutum mai son ci gaban al’umma wanda ya fifita ci gaban jama’arsa biye da komai. Ya kara da cewa ziyarar ta kara masa kwarin guiwa wajen cigaba da tsayawa tsayin daka akan duk abun ya shafi masu kananan karfi domin kawo dauki a rayuwarsu.

Don haka sai ya yi kira ga mahukuntan jami’ar ta MAUN da su duba lamarin cikin gaggawa domin a gaggauta fara aiki a harabar jami’ar ta Gwarzo, inda ya ce hakan zai rage matsalolin da dalibai ke fuskanta na neman gurbin karatu a jami’ar.

Cire T-Gwarzo Daga Minista Babban Kuskure ne – Kungiya Matasan APC ta Kasa

A jawabinsa tun da farko, Shugaban Jami’ar Maryam Abacha ta Najeriya (MAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayyana cewa sun je gidan Ministan ne domin jajanta masa kan abin da ya faru kwanan nan. Ya kuma yabawa tsohon Ministan bisa yadda ya yiwa al’ummar jihar Kano kyakkyawan wakilci a lokacin da yake kan mulki.

Farfesa Gwarzo, ya bayyana cewa tsohon Ministan ya cancanci a yi alfahari da shi a matsayinsa na wakilin al’ummar Kano, inda ya kara da cewa aikin kawo gidaje 500 a jihar ya isa a yaba da kokarinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...