Daga Isa Ahmad Getso
Dan majalisar tarayya mai wakilar karamar hukumar Dala a jihar kano, Aliyu Sani Madakin Gini ya bayyana ficewarsa daga tafiyar Kwankwasiyya dake biyayya da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Idan za a iya tunawa Aliyu Sani Madakin Gini na daga cikin na gaba-gaba a tafiyar Kwankwasiyya da yiwa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso biyayya.
Madakin Gini ya bayyana ficewarsa tasa ne daga tafiyar Kwankwasiyya da yammacin wannan rana ta lahadi a mazabar ta Dala dake jihar kano.

“Daga yau Ni Aliyu Sani Madaki na bar tafiyar Kwankwasiyya, Saboda Kwankwasiyya yaudara ce, Kwankwasiyya cin amana ce, Mai girma Gwamnan jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusif mutumin kirki ne, ina baka shawara ka tsaya da kafarka ka da aje fa ka wani rami da bazan bayyana shi yanzu ba”. Inji Ali Madaki.
Ya ce ya shirya tsaf domin tallafawa duk wanda ya biyo shi, yace kowa zai amfana, ya yi alkawarin zai share sama da Kwana 7 domin ganawa da magoya bayansa.
Ya umarci duk wani wanda ya yarda cewa shi ne Jagoransa, ya cire jar hula da jajayen mayafai.
Sai dai dan majalisar bai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP ba.