Rikicin PDP: Ibrahim Little da Wali sun zargi Shekarau da kassara Jam’iyyar a Kano

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Wani tsagi na jam’iyyar PDP reshen jihar Kano karkashin jagorancin Ibrahim Al’Amin Little da Sadiq Aminu Wali sun sha alwashin dawo da martabar jam’iyyar a jihar.

Ibrahim Little ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP dake fadin kananan hukumomi 44 na Kano.

Wannan mataki na daya daga cikin kokarin da tsagin ke yi na kara tabbatar da tasirinta da kuma dacewarsa a harkokin siyasar jihar.

Talla

Ya ce yunkurin da tsagin ke yi na farfado da martabar jam’iyyar PDP a Kano na da matukar muhimmanci, duba da irin gwagwarmayar da jam’iyyar ta yi a jihar Kano.

Cire T-Gwarzo Daga Minista Babban Kuskure ne – Kungiya Matasan APC ta Kasa

An zargi PDP a karkashin bangaren Malam Ibrahim Shekarau da haifar da rikice-rikicen da ba su dace ba wanda yace hakan ya jawo rabewar Jam’iyyar zuwa gida biyu.

Abubunwan da aka cimma a taron gwamnoni da Sarakunan Arewacin Nigeria

“Wannan taron da mukai wani bangare ne na matakan da muka fara dauka domin farfado da martabar jam’iyyar PDP a jihar”. Inji Little

Ya kara da cewa domin jaddada kudirinsu na tabbatar da akidu da kimar PDP, bangaren Little da Wali na da burin farfado da jam’iyyar a Kano da kuma kokarin ganin ta sami nasara a zabuka masu zuwa .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...