Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Kamfanin Mai na Nigeria NNPCL ya kara fitar da sabon farashin litar man fetur a Lagos inda ta karu zuwa N1,025, yayin da Abuja N1,050 duk lita.
Ƙarin farashin na zuwa yayin da ƴan Najeriya suka ƙauracewa sayan mai saboda tsadar da yayi tare da samun raguwar ababan hawa dake sufuri a biranan ƙasar.

Har wa yau ƙarin na zuwa yayin da wasu Alƙaluman da hukumar kula da albarkatun ruwa da kuma ƙarƙashin ƙasa a Najeriya suka nuna cewar an samu raguwar man da ake sha daga lita miliyan 60 a kowacce rana zuwa lita miliyan 4 da dubu 500 a 20 ga watan Agustan 2024.
Rikicin PDP: Ibrahim Little da Wali sun zargi Shekarau da kassara Jam’iyyar a Kano
Makonni uku da suka wuce, a ranar 09/10/2024, kamfanin mai na NNPCL ya kara farashin litar fetur daga Naira 897 a Abuja zuwa Naira 1,030 yayin da ya kai litar fetur din Naira 998 daga tsohon farashin Lagos din na Naira 885
Jaridar Daily Trust ta ce karin farashin da aka yi shi sau biyu cikin makonni uku ya biyo bayan daina biyan tallafin Naira 133 da NNPCL ke yi kan kowace litar fetur da aka sha a Nijeriya