Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce za a maido da wutar lantarki a jihohin Arewa 17 da suke fama da matsalar barna a layin Shiroro zuwa Kaduna nan da kwanaki biyar.
Mista Adelabu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan wata ganawa da yayi da shugaban kasa Bola Tinubu ranar litinin a Abuja.

Ya ce matsalar wutar lantarki da ake samu a yankin Arewacin kasar nan ya biyo bayan lalata layin Shiroro zuwa Kaduna da aka yi, babban layin da ke samar da wutar lantarki ga Arewa.
Sai dai ya ce za a gyara layin wutar a cikin kwanaki uku zuwa biyar.