Daga Sharifiya Abubakar
Gwamnatin jihar kano ta yi alkawarin hada kai da sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomin da Ake zaba domin kawo cigaba jihar Kano.
” Dama Muna yin aiyukan alkhairin yanzu kuma da aka zabi shugabanni za mu tabbatar mun hada kai da su domin kawo aiyukan cigaba a fadin jihar baki daya”.

Gwamna jihar Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan Jim kadan bayan kada kuri’arsa a zaben shugabannin kananan hukumomin da kansiloli a mazabar Chiranci dake kamar hukumar Gwale .
Ya ce gwamnatin jihar kano karkashin jagorancinsa za ta tabbatar da cewa sabbin Shugabannin kananan hukumomin sun yiwa al’ummarsu aiyukan cigaba.
Zaɓen kananan hukumomi: Kotu a Kano ta sake baiwa KANSIEC sabon umarni
” Waɗannan Yan takarar da ake zaba ko aka zaba sai da aka tsaya aka zabo masu nagarta don haka Ina baiwa al’ummar jihar Kano tabbacin za su yi aiyukan cigaba a dukkanin kananan hukumominsu”. Inji gwamnan
Ya Kuma ba da tabbacin cewa suna da matakai masu yawa da zasu ladabtar da duk wani shugabannin karamar hukumar da aka samu da almundahana da dukiyoyin al’ummarsa.

Gwamnan ya kuma yabawa al’ummar jihar Kano bisa yadda suka fito domin kada kuri’unsu a zaben shugabannin kananan hukumomin da kansiloli da Ake gudanarwa a dukkanin kananan hukumomi 44 daka jihar kano.