Matsayar gwamnatin Kano da martanin APC Kan zaɓen Kananan hukumomi

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta ce babu gudu babu ja da baya a zaben kananan hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar 26 ga watan Oktoba 2024.

Talla

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a wajen taron bada tutoci ga ‘yan takarar shugawagabannin kananan hukumomi 44 karkashin tutar jam’ iyyar NNPP wanda ya gudana a filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata cikin garin Kano

Gwamnana Abba Kabir ya buƙaci al’ummar jihar Kano da su fito kwansu da kwarkwata a ranar zabe domin zabar jam’iyyar NNPP .

Dambarwar Hisbah da Murja Kunya: Kotu ta yanke hukunci

” Babu wanda ya isa ya hana mu yin zabe, gwamnatin jihar kano ba ta yi kuskure ba haka suma shugabannin hukumar zabe da muka saka ba su yi kuskure ba, don haka uban kuturu yayi kadan ya hana mu yin zaben kananan hukumomi”. Inji gwamnan

Kazalika, Gwamnan ya kuma bayyana yakinin cewa jam’iyyar NNPP ce zata yi nasara a zaben bisa ganin yadda magoya bayan jam’iyyar daga kananan hukumomi 44 suka nu na halarci ga yan takarkarin su wajen taya su karbar tuta.

Zaɓen Kananan hukumomi: Hukumar zaɓe ta kano ta bayyana matsayarta kan hukuncin Kotu

Ya kara da cewa babu wani abu da zai basu tsoran fitowa zaben na ranar Asabar kuma babu gudu ba ja da baya kamar yadda suke kan turba gaskiya da rukon amana

Ya yin taron gwamna Abba Kabir Yusuf ya mikawa dukkanin yan takarar kujerun ciyamomi tutar jam’iyyar NNPP, wadda ke tabbatar da su a matsayin yan takarar jam’iyyar.

Sai dai a martanin ta ga kalaman gwamnan, jam’iyyar APC ta ce ba ta damu ba don gwamnatin jihar kano ta gudanar da zabenba, amma ya ce ita ma ba wanda zai hanata cigaba da bibiyar Shari’ar da ta shigar kan zaben.

Talla

Jam’iyyar APCn ta bayyana hakan ne ta bakin Kakakin jam’iyyar na jihar kano Ahmad Aruwa.

Ya ce ko da gwamnatin jihar kano ta yi zaben to su a ganinsu ta yi a banza, saboda za su kalubalanci hakan har zuwa kotun koli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...