An dakatar da Jaruma Halima Abubakar a masana’antar shirya fina finai ta Nijeriya

Date:

 

Kungiyar ‘Yan Wasan Fim ta Najeriya (AGN) ta dakatar da jarumar Nollywood Halima Abubakar saboda zargin bata suna.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na Instagram, ta bayyana cewa binciken da aka gudanar tsawon shekaru biyu ta hannun kwamitin da aka kafa ya nuna cewa Halima ta bata sunan wasu daga cikin abokan aikinta.

Talla

“Biyo bayan cikakken rahoton bincike na kwamitin Bincike na Musamman da aka kafa don gudanar da bincike a karkashin kasa game da ayyukan wasu shafukan yanar gizo tun daga 2022,” AGN ta rubuta.

Bincike ya gano adadin yawan yan Nigeria da suka talauce a bana

“Bayan shekaru biyu na bincike mai zurfi, Kwamitin ya gano cewa Halima Abubakar ce ke da alhakin dukkan bayanan bata suna na mambobinmu, abokan huldarmu, da masu tallafa mana, musamman labaran da suka shafi alakar saduwa da aka alakanta da mutane masu kima a cikin al’umma daga masana’antar.”

Kungiyar ta ce, duk da dakatarwar da aka yi wa Halima, har yanzu za ta fuskanci matakan ladabtarwa.

Talla

“Saboda haka, Halima Abubakar an dakatar da ita ba tare da iyaka ba daga Kungiyar ‘Yan Wasan Fim ta Najeriya. Za ta fuskanci Kwamitin Ladabtarwa na Kasa don yanke hukuncin da ya dace. A lokacin wannan dakatarwar, ba a ba ta damar shiga cikin kowanne irin aiki na AGN ko kuma aikin fim.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...