Minista Gwarzo ya bi sahun Yan ƙasar Spain wajen bikin ranar kasar ta bana

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane na kasa, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya bi sahun al’ummar kasar Spain mazauna Najeriya domin gudanar da bikin ranar kasa ta Spain ta bana (2024) a wata liyafa da ofishin jakadancin kasar ya shirya a Abuja.

Tun da farko, a cikin wata wasikar taya murna da ministan ya aikewa jakadan kasar Spain a Najeriya, Juan Ignacio Sell, ya bayyana cewa dadewar dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Spain ta haifar da fa’ida da dama ga kasashen biyu.

Talla

Minista Gwarzo, ya yabawa ‘yan kasar Spain bisa yadda suke kiyaye dimbin al’adunsu da ya ce sun taimaka wajen samun ci gaban kasar, ya kara da cewa taron tunawa da ranar kasa ya kara fito da kimar kasar da ‘yan kasar ta Spain .

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimakawa ministan kan harkokin yada labarai Adamu Abdullahi ya aikowa kadaura24.

Talla

Ya nemi karin hadin gwiwa tsakanin Spain da Najeriya, musamman a fannin gidaje da raya birane. “Ina fatan kara karfafa dangantakarmu yayin da muke kokarin samar da mafita mai dorewa a birane wanda zai zama mai amfani ga kasashen biyu,” in ji Ministan.

A yayin liyafar da aka gudanar a ofishin jakadancin kasar Spain, Jakadan kasar Spain a Najeriya, Juan Ignacio Sell, ya bayyana jin dadin kasarsa bisa yadda minista Abdullahi Tijjani Gwarzo ya zama abokin kasar Spain.

Talla

Ya kuma yaba da dangantakar diflomasiyya da ke tsakanin Najeriya da kasarsa. Mr. Sell ya ce kasashen biyu za su ci gaba da yin aiki tare domin cimma burin jama’arsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related