Zargin almundahana: An kulle Janar din Soja dake aiki a Kano bisa zargin karkatar da Shinkafa da sayar da kayan aiki

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

 

An tsare kwamandan rundunar sojoji ta 3 dake Kano, Birgediya Janar M.A. Sadiq, bisa zargin karkatar da tallafin shinkafa, da sayar da kayan aikin soja da suka hada da na’urar janareta da motocin aiki.

Wasu majiyoyin da suka zanta da jaridar DAILY NIGERIAN bisa sharadin sakaya sunansu, sun ce hedkwatar tsaron Najeriya ta ba da shinkafar ga sojoji a duk fadin kasar domin rabawa jami’an sojoji a matsayin kayan tallafi .

Talla

An rawaito cewa hedkwatar tsaro ta raba shinkafar a kalla sau uku ga sojojin Najeriya, don saukaka musu.

Amma rahotanni sun nuna cewa Janar din da aka kullen din sau daya kawai ya rabawa sojojin dake karkashinsa shinkafa mai nauyin 5kg, ya kuma sayar da sauran.

An baiwa Ganduje wa’adin Kwanaki 7 ya sauka daga mukamin shugaban APC na Ζ™asa

Baya ga badakalar shinkafa, jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa Janar din ya kwashe kayan aiki da suka hada da janareta MIKANO, dake sansanin horas da sojoji dake Falgore a Kano ya sayar da su ga yan Gwan-gwan.

Daily Nigerian ta tabbatar da cewa an maye gurbin jami’in sojan da wani tsohon magatakarda na makarantar horas da sojoji ta Najeriya Birgediya Janar A.M. Tukur.

β€œBayan wadannan zarge-zarge, an tsare Birgediya Janar Sadiq a dakin gadi, kuma yana fuskantar bincike daga sashin bincike na musamman na β€˜yan sandan sojoji a Abuja.

Talla

β€œDa farko an gayyace shi Abuja domin yi masa tambayoyi, kuma nan take aka ba da umarnin a kulle shi a dakin gadi na β€˜yan sandan sojoji, domin cigaba da bincike.

 

β€œAna ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan lamarin. Watakila zai fuskanci tuhuma a kotun soji,” majiyar ta kara da cewa.

Don Jin tabakin rundunar sojojin, majiyar kadaura24 ta tuntubi Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, amma bai amsa kira da sakon SMS da aka aika masa ta lambar wayarsa da aka sani ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related