Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, a ranar Lahadi, ya ce sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Ribas ya kawo karshen cin zarafi da siyasar ubangida a jihar.
Atiku ya ce wannan zai da damar yiwa al’umma aiki yadda ya dace kuma damar bin kundin tsarin mulki a jihar.

Ya yabawa gwamna Sim Fubara na jihar Ribas kan sakamakon zaben kananan hukumomin da aka kammala a jihar.
A 2027 za mu sallami Kwankwaso daga Siyasa – Doguwa
Atiku ya ce sakamakon zaben ya nuna cewa Fubara ya nuna jajircewarsa ga muradun jama’a da kuma kare martabar zaben kananan hukumomi.

Sanarwar da Atiku ya sanyawa hannu ta ce: “A yayin da aka kammala zaben kananan hukumomi a jihar, an kawo ƙarshen tsoratarwar da ake yiwa gwamnan, wanda hakan zai ya bayar da damar fara gudanar da kyakkyawan shugabanci a jihar.