Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama mutane 89 da ake zargi da aikata laifuka

Date:

 

 

Rundunar ‘yansandan jihar ta kama mutane 89 bisa zargin aikata laifuka daban-daban, a kokarin ta na magance ayyukan bata gari a jihar Kano

Kwamishinan ‘yansandan jihar, Salman Dogo ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai jawabi a shelkwatar rundunar dake Bompai, Kano a ranar Litinin.

Talla

Dogo ya ce laifukan da mutanen suka aikata sun hada da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Ya ce, an yi kamen ne a wurare daban daban na jihar, daga ranar 12 ga watan Satumba zuwa yau inda ya kara da cewa an mika mutane 53 da ake zargi gaban kotu a yayin da 36 ake kan bincike a kansu.

Kamfanin Gerawa ya fara biyan ma’aikatansa mafi ƙarancin albashin N70

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin SP, Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar, ya ce an kwato makamai masu hatsari daga wajen wadanda ake zargin da suka hada da bindiga da adda da wukake.

Talla

Sannan ya ce rundunar za ta ci gaba da aiwatar da aikin ta kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

“A don haka, rundunar ‘yansanda zata ci gaba da sauke nauyin dake kanta kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada”, inji Kwamishinan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...