Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa, ya bayyana shirin kafa cibiyoyin maida ababen-hawa zu zama masu amfani da iskar Gas (CNG) a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.
Namadi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Hamisu Gumel, ya fitar a yau Alhamis a Dutse.

Gwamnan wanda ya yi magana a wajen kaddamar da wani gidan mai na Safa and Fresh International Limited a jiya Laraba a Dutse, ya ce za a kafa cibiyoyin na CNG ne tare da hadin gwiwar kamfanin.
Gwamnatin Kano ta ciyo bashin makudan kudade don inganta ruwan sha
Namadi ya ce kafa cibiyoyin CNG zai rage kashe kudade da ake wajen sayen man fetur da kashi 60 cikin 100, inda ya kuma kara da cewa hakan zai taimaka matuka ga mazauna jihar.

Ya ce shirin zuba jarin ya yi dai-dai da ajandar gwamnatinsa guda 12, da nufin samar da ayyukan yi da bunkasar tattalin arziki.
Daily Nigerian