Rasuwar yan sandan Kano babban rashi ne ga Nigeriya – Sarki Aminu Bayero

Date:

Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana rasuwar jami’an ‘yan sanda biyar da cewa wani babban rashi ne, ga ƙasar nan baki daya.

 

Idan za’a iya tunawa jami’an yan sanda guda 5 sun rasa rayukansu, sannan wasu guda goma sha daya da suka samu raunuka sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a garin karfi dake kan titin Kano zuwa Zaria da a safiyar yau Talata.

Talla

Mai Martaba Sarkin yace Rasuwar jami’an ‘yan sanda a bakin aikinsu wani babban lamari ne mai ban tausayi da ban tsoro, duba da irin gagarumar rawar da ‘yan sanda ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma musamman ma kasa baki daya.

Dalilin da ya sa ‘yan kasuwar mai a Nigeria suka gwammace sayan man a NNPCL maimakon matatar Dangote – PENGASSAN

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran sarkin Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace sarkin ya ce ayyukan da suke yi na cike da sadaukarwa ga al’umma wanda ya baiwa ‘yan kasa damar gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana.

Talla

Alhaji Aminu Ado Bayero data nan said ya mika ta’aziyyar sa ga babban sufeton ‘yan sanda na Kasa, da Mataimakinsa Mai Kula da shiya ta daya dake Kano da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, da iyalai da ‘yan uwan ​wadanda suka rasu tareda yin addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu yasa sun huta.

Ga wadanda suka jikkata kuwa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi addu’ar samun sauki cikin gaggawa daga raunukan da suka samu da kuma kiyayewar faruwar haka nan gaba.

Talla

Daga nan sai sarkin ya shawararci Jama’a musamman masu ababen hawa da masu amfani da ababen hawa da su rika kiyaye ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa a kodayaushe kan manyan hanyoyi domin ci gaba da ceto rayukan ‘yan kasar da faduwar haddura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...

Neman Ilimin addini dana boko da sana’a ba kishiyoyin juna ba ne – Dr. Aminu Sagagi ga matasan Zango

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malamin addinin musulunci a kano...