Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukunci a karar nemen tsige Ganduje daga shugabancin APC na ƙasa

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

 

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da ke neman a tsige Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Mai shari’a Inyang Ekwo, a hukuncin da ya yanke, ya yi watsi da karar a kan cewa wadanda suka shigar da karar, kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya, karkashin jagorancin Alhaji Saleh Zazzaga, ba ta da wata hujja kan da’awarsu.

Mai shari’a Ekwo, wanda ya ce ba a gabatar da sahihiyar shaida a gaban kotun ba da ke nuna cewa kungiyar na da rajista da Hukumar Kula da Kamfanoni ta kasa ba wato CAC , sannan ya ce doka bata san da kungiyar ba.

Nasarar APC a zaɓen Edo ta nuna yan Nigeria sun gamsu da salon mulkina -Tinubu

Alkalin ya ci gaba da cewa kungiyar ba ta da hurumin shigar da karar saboda batun da suka gabatar a gaban kotun ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar APC.

Ya ce za a iya nadawa ko tsige shugaban jam’iyyar na kasa ta hanyar babban taronta na kasa.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta A ranar 18 ga watan Satumba ne mai shari’a ya sanya yau litinin a matsayin ranar yanke hukunci kan karar.

Talla

Wanda ya shigar da karar, kungiyar APC ta Arewa-Tsakiya, ta shigar da karar ne domin neman cire Ganduje daga matsayin shugaban jam’iyyar APC saboda shi ba dan shiyyar Arewa ta tsakiya ba ne.

A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/599/2024, masu shigar da karar sun bayyana Ganduje da APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta a matsayin wadanda ake kara na daya zuwa na uku.

Masu karar sun bukaci kotun ta hana Ganduje ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...