Zaɓen Edo: Magoya Bayan PDP Sun Fara Zanga-Zanga

Date:

 

Magoya bayan Jam’iyyar PDP, sun fara zanga-zanga yayin da ake dakon sakamakon ƙananan hukumomi biyu da suka rage a Zaɓen Gwamnan Jihar Edo.

Jam’iyyar APC, wadda ita ce babbar jam’iyyar adawa a Edo, tana kan gaba a zaɓen bisa sakamakon da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana.

Hanya ɗaya tak da za a inganta rayuwar yaran da ke barace-barace a Kano da Arewa – Daga Mustapha Hodi Adamu

Magoya bayan PDP, sun mamaye hedikwatar INEC da ke birnin Benin, don yin zanga-zanga kan sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar, wanda har yanzu ake ci gaba da ƙirga ƙuri’u.

INEC, ta dakatar da bayyana sakamakon bayan ta bayyana sakamakon ƙananan hukumomi 16 daga cikin 18 da ke jihar.

A halin yanzu, APC ta yi nasara a ƙananan hukumomi 10, yayin da PDP ta yi nasara a ƙananan hukumomi guda shida.

Talla

Ana sa ran INEC za ta sanar da sakamakon sauran ƙananan hukumomi biyu da suka rage a yammacin ranar Lahadi.

Tun da farko daily trust, ta ruwaito yadda APC ta kasance a kan gaba da ƙuri’u 244,549, sai PDP da ƙuri’u 195,954, yayin da jam’iyyar LP ke da ƙuri’u 13,348.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...