Za mu hada hannu domin inganta kasuwar wayar hannu ta Farm Center – Amb. Jamilu Bala Gama

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Sabon shugaban kasuwar wayar hannu ta farm center dake jihar kano a Arewacin Nigeria ya sha alwashi hada hannu da masu ruwa da tsaki da al’ummar kasuwar wajen kawo cigaban da kowa zai alfahari da shi.

“Babu wani shugaba da zai yi nasara ba tare da goyon bayan wadanda yake shugabanta ba, don haka zamu bar kofarmu a bude don karbar shawarwarinku da kuwa gyara idan Mun yi kuskure a matsayinmu na yan Adam”.

Sabon shugaban kasuwar ya bayyana hakan ne cikin wani sakon da ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Hukumar Shari’a a Kano ta dakatar da ma’aikatan kotu kan badaΖ™alar filaye

A sakon Amb. Jamilu Bala Gama ya ce zai duk mai yiwuwa wajen fito da managartan tsare-tsaren da ya tsara domin ciyar da kasuwar wayar hannu ta farm center gaba.

Talla

Ya bukaci al’ummar kasuwar su ba su hadin kai da goyon baya don ciyar da kasuwar gaba.

” Ina godiya ga wadanda suka ba ni gudunmawa na zama shugaban wannan kasuwa musamman mai girma gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da kwamishinan Kasuwanci na kano da dan takarar shugaban karamar hukumar Birni a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Boye da duk matasa da Dattawan kasuwar wayar hannu ta farm”. A cewar Jamilu Bala Gama

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related