Nema yafiya:Bafarawa ya baiwa mutanen sokoto Naira Biliyan 1

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayar da gudummawar Naira biliyan 1 a matsayin tallafi ga al’ummar jihar a ranar larabar nan.

Kadaura24 ta rawaito Bafarawa ya mulki jihar na tsawon shekaru takwas, tsakanin 1999 zuwa 2007.

Ya bayyana cewa ya bada tallafin ne domin cikar burinsa na ganin ya cike duk wani gibi da ya haifar a yayin da yake kan karagar mulki.

Badakalar magunguna: Kananan hukumomin Kano sun yi karar shugaban ICPC na kasa

“A matsayina na Dan shekaru 70 da haihuwa, bana jin dadin Inga mutane cikin kunci. Burina a yanzu shi ne in tabbatar da cewa na cike duk wani gibi da na iya haifar, Ina sane ko cikin rashin sani lokacin da nake mulki domin kara kyautata dangantakara da jama’a .

“Wasu na iya kiran wannan abu da nayi a matsayin kaffara, amma na fi son mutane su sani ni na dauke shi a matsayin wani aiki na biyan bashi. Ina so in sakawa mutane saboda irin ƙaunar da suka nuna mini”. Inji Bafarawa

Kamaru ta buɗe Madatsar Lagdo: Jihohin 11 Najeriya su shirya wa ambaliya —Gwamnatin Nigeria

“A bisa wannan dalili ne na yanke shawarar samar da zunzurutun kudi har N1bn domin jin dadin jama’ar jihar Sokoto,” in ji shi.

Sai dai ya nemi gafarar jama’a bisa duk wani laifi da ya aikata a lokacin da yake gwamnan jihar.

Bafarawa ya bayyana cewa an damka rabon kuɗin a hannun wani kwamiti dake karkashin jagorancin Malam Lawal Maidoki, shugaban hukumar zakka ta jihar Sokoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...