EFCC ta ce Yahaya Bello ba ya hannunta

Date:

 

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta ƙaryata iƙirarin da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi na cewar ya amsa goron gayyatar da ta aike masa.

Hukumar ta bayyana cewa har yanzu tana neman tsohon gwamnan bisa zargin karkatar da Naira biliyan 80.2.

Kakakin hukumar, Dele Oyewale ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aike wa ’yan jarida a ranar Laraba

Nema yafiya:Bafarawa ya baiwa mutanen sokoto Naira Biliyan 1

Tun da farko, ofishin yaɗa labaran Bello, ya fitar da wata sanarwa da safiyar ranar Laraba, inda ya ce tsohon gwamnan ya yanke shawarar amsa gayyatar EFCC bayan tattaunawa da iyalansa da lauyoyinsa.

Ofishin ya kuma yi alƙawarin yin cikakken bayani game da ganawar Bello da EFCC nan gaba.

Sanarwar, wanda Daraktan Ofishin Yaɗa Labaran Yahaya Bello, Ohiare Michae, ya sanya wa hannu, ta kuma buƙaci EFCC ta kasance mai ƙwarewa da mutunta haƙƙin tsohon gwamnan a matsayinsa na ɗan ƙasa.

Kamaru ta buɗe Madatsar Lagdo: Jihohin 11 Najeriya su shirya wa ambaliya —Gwamnatin Nigeria

Amma da yake mayar da martani kan iƙirarin, kakakin hukumar ya ce babu yadda za a aike wa mutumin da ake nema ruwa a jallo, goron gayyata.

Oyewale ya ce, “Rahotannin da ke yawo cewar Yahaya Bello yana hannun EFCC ba gaskiya ba ne.

Hukumar tana son bayyana cewa Bello ba ya hannunta. Ana ci gaba da neman shi kan zargin karkatar da Naira biliyan 80.2, tare da sammacin kama shi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...